Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da dokar kafa Jami’an tsaron jiha

Majalisar jihar Kano
Majalisar jihar Kano

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da dokar, kafa rundunar tsaro ta jiha domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Amincewar ta zo ne bayan wata zazzafar muhawara kan wasu sassa na dokar, wadda ta tanadi hana duk wani wanda ke cikin jam’iyyar siyasa jagorantar rundunar.

Shugaban masu rinjaye na majalisar, Honarabul Lawan Hussaini Dala, ya bayyana cewa an yi nazari sosai kan dokar don tabbatar da cewa tana da amfani ga kowane ɓangare na jihar.

dokar ta ba wa jami’an rundunar ikon ɗaukar makamai, cafke masu laifi da kuma hana aikata miyagun ayyuka, domin kara tabbatar da tsaron rayuka da kuma dukiyoyin al’umma a lungu da sako na jihar Kano.

A ƙarshe Dala ya tabbatar da cewa wanda zai jagoranci rundunar dole ne ya kasance ɗan jihar Kano kuma ba dan wata jam’iyyar siyasa ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com