Gwamnatin Najeriya ta sanar da shirin ci gaba da rike ma’aikatan lafiya 28,000 da Hukumar Raya Kasashe ta Amurka USAID ke daukar nauyinsu a baya, wanda shugaban Amurka Donald Trump ya dakatar da ayyukanta.
Read Also:
Ministan lafiya da walwalar jama’a na Najeriya, Muhammad Pate, ya bayyana hakan, yayin hira da wata kafar talabijin ta ƙasar, inda ya bayyana cewa gwamnati na ƙoƙarin shigar da ma’aikatan cikin tsarin kiwon lafiyar ƙasar tare da rage dogaro da tallafi da ƙasashen ƙetare ke bayarwa.
Mista Pate ya bayyana gagarumar gudunmawar da gwamnatin Amurka ke bayarwa a fannin kiwon lafiyar Najeriya, musamman a bangaren cutar kanjamau, tarin fuka, da zazzabin cizon sauro, sai dai ya jaddada cewa Najeriya ta kuduri aniyar daukar nauyin sashen kula da lafiyarta da kuma rage dogaro da tallafin da take samu daga waje.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1463 days 15 hours 28 minutes 54 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1445 days 17 hours 10 minutes 19 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com