Tinubu ya ayyana ranar hutun ma’aikata

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Alhamis a matsayin ranar hutu domin baiwa ma’aikata damar gudanar da bikin ranar ma’aikata ta bana, wadda ake gudanarwa duk ranar 1 ga watan Mayu na kowacce shekara.

Olubunmi Tunji-Ojo, ministan harkokin cikin gida ne ya sanar da hutun a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata.

Gwamnatin Kano ta shiryawa Limaman masallatan juma’a Bita

Tunji-Ojo ya yabawa ma’aikatan Najeriya bisa jajircewa da sadaukarwar da su ke yi, wajen ganin kasar ta samu cigaban da ake fata .

Ya bukaci ma’aikatan Nijeriya da su za mo masu dabi’ar kirkira da yin aiki mai inganci don cigaban tattalin arzikin Nigeria.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com