Home General ‘Yanbindiga sun sace mutum 117 da hallaka wasu tara a Jihar Kebbi

‘Yanbindiga sun sace mutum 117 da hallaka wasu tara a Jihar Kebbi

Rahotannin daga Nijeriya na bayyana cewa wasu ‘yanbindiga sun hallaka akalla mutane tara sannan kuma suka yi awon-gaba da wasu magidanta 117, a garin Danmuntari da ke yankin Danko-Wasagu a jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin kasar.

Wasu mazauna garin da suka tsira daga harin sun tabbatar wa da BBC, cewa lamarin ya faru ne a yammacin ranar Talata, 27 ga watan Mayun, 2025, lokacin da ‘yanbindigan su ka yi wa garin kofar-rago.

Daga cikin wadanda barayin dajin suka kashe har da wata mata mai jego da jaririnta, inda suka harbe su tare da sauran jama’ar da suka hallaka ta hanyar harbin kan-mai-uwa-da-wabi a lokacin da suka shiga garin, kamar yadda shedun suka yi bayani.

”Da la’asar barayin suka kewaye garin suka dinga harbe-harbe wanda hakan ya sa dole mutanen garin suka watse suka cimma na kashewa, suka kashe mutum tara,”in ji daya daga cikin mutanen garin.

Ya kara da cewa, ”Abin ban tausayi akwai mace daya da ba ta wuce sati biyu da haihuwa ba suka kashe ta da ita da jaririnta.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp