BINCIKE: Shin da gaske ne an taɓa Daukar Hoton tsohon shugaban Nijeriya Janar Sani Abacha da Peter Obi suna shan shayi a Fadar Shugaban Kasa?
IKIRARI: Wani hoto da ke yawo a kafafen sada zumunta na zamani, musamman a shafin X, na iƙirarin cewa, tsohon gwamnan jihar Anambra kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a 2023, Peter Obi yana shan shayi tare da marigayi Janar Sani Abacha, tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya, a Fadar Shugaban Kasa.
Sakon da ke tare da hoton ya na dauke da kalmomin masu jan hankali da ke cewa: “Wani hoto na ban mamaki na Peter Obi da Janar Sani Abacha suna shan shayi tare a Fadar Shugaban Kasa. Daya daga cikin wadanda suka kashe dimokuradiyya a 12 ga Yuni yanzu yana kokarin zama dan dimukradiyya!!!”
Hoton ya nuna wasu mutane biyu zaune a wajen da ke da kama da ofishin gwamnati; daya sanye da kayan farar hula, dayan kuma da kayan soji a jikinsa, a bayan su kuma ga tutur Nijeriya a bango — abin da ke nuna alamar a Fadar Shugaban Kasa ne.
Wannan hoto ya samu karbuwa cikin gaggawa a kafafen sada zumunta, musamman daga masu bibiyar harkokin siyasa, inda da dama suka dauke shi a matsayin yunƙuri na shafa wa Peter Obi kashin kaji dangane da rawar da ake zargin ya taka a mulkin Abacha. Haka kuma lamarin yazo a kan gaba daidai lokacin da ake ta tattaunawa game da zargin Obi yana da alaka da gwamnatin Abacha, wanda ya musanta kwanan nan ta hanyar wata takarda don fayyace matsayinsa.
Janar Sani Abacha ya mulki Najeriya daga 1993 zuwa 1998 lokacin da ya rasu. A ‘yan tsakanin nan, tsohon shugaban kasa Janar Ibrahim Babangida ya dora masa laifin rushe sakamakon zaben 1993 da ake ganin MKO Abiola ne yayi nasara, da kuma zargin cin zarafin dan Adam a lokacin da yake mulkar kasar.
Peter Obi ya fara siyasa ne shekaru bayan mulkin Abacha, inda ya lashe zaben gwamna na farko a 2003 (ya shiga ofis a 2006 bayan shari’o’i).
Tabbatarwa: Tawagar bincike ta PRNigeria ta gudanar da cikakken bincike domin tabbatar da sahihancin hoton da kuma gaskiyar iƙirarin. Binciken da aka gudanar ta amfani da kayan aikin tantance hotuna da binciken hoto ta hanyar “reverse image search” ya gano alamu da dama da ke nuna cewa hoton an kirkire shi ne ta hanyar amfani da na’ura.
Read Also:
Binciken ya bayyana cewa babu wata hujja mai karfi daga kundin tarihi da ke nuna cewa mutanen da ke hoton su ne Peter Obi da Janar Sani Abacha.
Hakanan, ba a taba samun rahoton wata ganawa tsakaninsu ba daga wata kafar labarai mai inganci ko daga wata majiya ta hukuma.
Hoton na da launin sepia da kuma karancin inganci, sannan kamar an daidaita shi ta hanyar kwaikwayo, wanda hakan ke kara nuna cewa hoton ba na gaskiya ba ne. Binciken ya kuma gano cewa hoton ya fara yaduwa ne a kafafen sada zumunta a ranar 10 ga Yuli, 2025.
Ƙarin Bayani: A cikin martanin da ya bayar dangane da zargin cewa yana da alaka da gwamnatin Abacha, Peter Obi ya saki wata wasika da aka ce ta fito daga 1996, wadda ke nuna cewa an nada shi a wani kwamitin wani kamfani mai zaman kansa, ba na gwamnati ba.
A cewarsa, “Kamar yadda na bayyana a wata hira da aka yi da ni a karshen mako, ban taba haduwa da Janar Sani Abacha ba kafin wannan lokaci,” in ji Obi.
“Muna tare da wasu ‘yan kasuwa ne muka je wurinsa don nuna damuwa kan tsaikon da ake samu wajen karbar kaya a tashoshin jiragen ruwa. Ba a matsayin ‘yan siyasa muka je ba, sai dai a matsayin ‘yan kasa masu kishin kasa da ke son a magance matsalar da ke shafar tattalin arziki da rayuwar jama’a.”
Ya kara da cewa wannan ganawa ba ta da alaƙa da siyasa ko wani mukami daga gwamnatin mulkin soja.
kuma Irin wannan hoton da aka ce na bogi ba sabon abu ba ne — an taɓa yada wani hoto makamancin haka da ya nuna Bola Tinubu tare da Abacha, wanda shima babu wata sahihiyar majiya da ta tabbatar da gaskiyar hoton.
Binciken PRNigeria ya kuma gano wasu kurakurai a cikin hoton. Misali, tambarin da ke kan hular Janar Abacha bai dace da wanda sojojin Najeriya ke amfani da shi ba. Hakanan, alamomin matsayin soja (epaulettes) da ke kafaɗarsa ba su daidaita da na gaske. Haka kuma, Abacha yana da alamun fuskarsa (tribal marks) da suka bace a hoton.
Kammalawa: Binciken PRNigeria ya gano cewa babu wata sahihiyar shaida da ke nuna cewa an taɓa daukar hoto na Peter Obi da Janar Sani Abacha suna shan shayi tare a Fadar Shugaban Kasa. Hoton na karya ne, kuma an kirkire shi ne da alama domin biyan wata bukatar siyasa.
Hukunci: An yada hoton ne domin rudar da al’umma
Daga PRNigeria.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1495 days 7 hours 32 minutes 39 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1477 days 9 hours 14 minutes 4 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com