Home General Atiku Abubakar ya magantu kan tsare Tambuwal da EFCC ta yi

Atiku Abubakar ya magantu kan tsare Tambuwal da EFCC ta yi

Tsohon ɗantakarar shugabancin Najeriya, Atiku Abubakar, ya ce kamawa da tsare tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal da EFCC ta yi na da alaƙa shigarsa cikin haɗakar jam’iyyun hamayya.

Atiku ya bayyana haka ne a shafinsa na Facebook, inda ya zargi gwamnatin Tinubu da yunƙurin cin zarafi da tsoratarwa da nufin murƙushe jam’iyyun hamayya a ƙasar.

“Abun da muke gani a yanzu shi ne yadda gwamnatin Tinubu ke amfani da yaƙi da cin hanci a matsayin karen farauta domin daƙile jagororin jam’iyyun hamayya tare da jan su zuwa jam’iyya mai mulki.”

Ya ce abin da ke faruwa ba ya cikin, “manufarmu a lokacin da muka yi aiki tuƙuru domin assasa hukumar EFCC. Yanzu abubuwa na fitowa fili cewa duk wani ɗansiyasa da ke da alaƙa da jam’iyyun adawa yana fuskantar barazanar zargin cin hanci da rashawa, amma da zarar sun koma jam’iyya mai mulki, sai a ‘yafe’ musu.”

Atiku ya ce duk da cewa yaƙi da cin hanci da rashawa lamari ne da ke buƙatar goyon bayan ƴan Najeriya, ya ce haɗa yaƙin da wata manufa ta daban abu ne da ya cancanci suka daga ƙungiyoyi gwagwarmaya da ma ƙasashen duniya masu ƙawance da Najeriya.

A ƙarshe Atiku ya ce yana ba ƴan Najeriya tabbacin cewa za ba su yi shiru su zura ido suna gani ana ɗaukar matakai da suke barazana ga dimukuraɗiyyar ƙasar ba, wadda ya ce ana yunƙurin mayar da ita siyasar jam’iyya ɗaya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp