NDLEA ta kama wani matashi da yayi safarar kwayoyin Tramadol dubu 7 daga Legas zuwa Kano

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa reshen jihar kano ta tabbatar da kama wani matashi da take zargi da safarar kwayar Tramadol dubu 7 daga jihar legas zuwa kano.

Wannan na cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar ASN Sadiq Muhammad Maigatari ya aikewa PRNigeria a safiyar litinin 25 ga watan Agustan 2025, a madadin kwamandan rundunar ta jihar Kano.

Sanarwar ta ce Jami’an hukumar dake kiru sun sami nasarar kama wani matashi mai suna Adamu Yusuf dan shekara 29 a ranar 23 ga watan agusta a Kwanar Dangora akan hanyar sa ta shigowa Kano daga Legas dauke da kwayoyin.

Wanda ake zargin ya zuba kwayoyin da nauyin su ya kai kilogram 4.1, ne cikin wata jarkar Mai mai daukar lita 25, wannan ya nuna kokarin da hukumar ta ke na yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi a Nijeriya.

daga bisani sanarwar ta yabawa jamián hukumar bisa kokarin da suka nuna, tare da yin kira da Alúmma wajen basu dukkan gudunmawar da ta kamata domin gudanar da ayyukansu na yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi a jihar Kano da Nijeriya baki daya

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com