Gwamnan jihar kebbi ya amince da naɗin sabon sarkin Zuru

Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris ya amince da nadin Alhaji Sanusi Mika’ilu a matsayin sabon sarkin Zuru.

Cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamnan, Ahmed Idris ya fitar ya ce gwamnan ya amince da naɗin ne sakamakon shawarar kwamitin zaɓen sabon sarkin.

Yayin da yake miƙa wa sabon sarkin takarakar nadin kwamishin ƙananan hukumomi da masarautun gargajiya na jihar, Hon. Garba Umar Dutsin-Mari ya buƙaci sabon sarkin ya nuna halin dattakon da aka tsammata daga gare shi.

Naɗiin sabon sarkin na zuwa ne bayan mutuwar tsohon sarkon Marigayi, Alhaji Muhammad Sani Sami wanda ya rasu ranar 16 ga watan Agustan da muke ciki.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com