
Gwamnatin jihar Neja da ɗora wa makarantar St Mary alhakin sace ɗaliban makarantar da ƴan bindiga suka yi a tsakar daren jiya Alhamis.
Cikin wata sanarwa da gwamnatin ta fitar, ta ce rashin bin shawarar da ta bayar ne ya haifar da matsalar.
‘Dama tuni mun samu bayanan sirri game da barazanar tsaro a yankin – da ke yankin arewacin jihar, lamarin da ya sa muka ɗauki matakin rufe duka makarantun kwanan da ke yankin tare da dakatar da ayyukan gine-gine”. in ji sanarwar.
Sanarwar ta ci gaba da cewa amma abin kaico sai hukumomin makarantar St. Mary suka yi gaban kansu suka sake buɗe makarantar ba tare da sanar da gwamnati ko neman sahalewa ba, inda suka jefa rayukan ɗalibai da malaman makarantar cikin hatsari.
Gwamnatin ta ce tuni ta ƙaddamar da bincike da ƙoƙarin kuɓutar da ɗaliban tare da maido da su cikin kwanciyar hankali.
”Gwamnatin jihar Neja na tuntuɓar jami’an tsaro kan matakan da ake ɗauka na kuɓutar da ɗaliban”, in ji Sanarwar.
Harin na zuwa ne kwana biyar da sace ɗaliban makarantar sakandiren ƴanmata da ke garin Maga a jihar Kebbi tare da sace ɗalibai fiye da 20.










