Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kuɗi na 2023 da ya kai naira tiriliyan 19.76 a gaban gamayyar majalisun dokokin Nijeriya a ranar Juma’a.
Kasafin shi ne na ƙarshe da shugaban ya gabatar yayin da yake shirin kammala wa’adin mulkinsa na biyu a ranar 29 ga watan Mayun 2023. Buhari yace yana son ya bar abin tarihi a kasar fiye da yadda ya same ta a 2015.
Wannan ne kasafin kuɗi mafi yawa a tarihin Najeriya, inda ya zarta na shekarar 2022 da kashi 15.37 – wanda aka gabatar kan naira tiriliyan 17.13.
Read Also:
Kasafin kuɗin yana da giɓin da sai gwamnati ta hada da rance za ta cike fiye da rabin sa, wanda ya kai tiriliyan 12.
Gwamnatin tarayyar Nijeriyar ta bakin Ministar Kuɗi Zainab Shamsuna ta ce za ta cike giɓin ne ta hanyar ciyo bashi da kuma sayar da wasu kadarorin gwamnati.
Kazalika akwai batun tallafin man fetur, wanda shi ma ƙarin dawainiya ne ga kasafin, wanda zai iya janyo zazzafar muhawara, kasancewar wasu na goyon bayan gwamnati ta ci gaba da ba da shi, yayin da wasu ke ganin ya kamata a dakatar, saboda a nasu ra’ayin masu hada-hadar man sun fi talaka cin gajiyar tallafin.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 19 hours 48 minutes 50 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 21 hours 30 minutes 15 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com