Buhari ya Amince da kafa Kwamitin shirye-shiryen Mika mulki

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da nadin kwamitin shirye-shiryen mika mulki na ofishin shugaban kasa, wanda zai gabatar da dukkan ayyukan shirin mika mulki ga sabuwar gwamnatin da za ta gaji wannan bayan zaben 2023.

Wannan na cikin wata sanarwa da Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya ya fitar da sa hannun Willie Bassey wanda shi ne daraktan yada labarai a ofishin.

Ga mambobin kwamitin:

1. Sakataren Gwamantin Tarayya – Shugaban kwamitin 2. Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya 3. Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma babban sakatare a ma’aikatar shari’a 4. 

Manyan sakatarori daga wadannan ma’aikatun gwamnatin tarayya:

  • Tsaro
  • Harkokin Cikin Gida
  • Kudi da Kasafi da Tsare-tsare
  • Harkokin Waje
  • Yada Labarai da Al’adu
  • Babban Birnin Tarayya (FCTA)
  • Ayyuka na Musamman
  • Ofishin Shugaban Kasa, karkashin Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya
  • Ofishin Ayyukan Yau da Kullum karkashin Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya
  • Ofishin kula da Tattalin Arziki da na Siyasa, karkashin Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya
  • Fadar Shugaban Kasa

5. Ofishin Mai ba Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro

6. Hafsan Hafsoshin Sojojin Najeriya

7. Sufeto-Janar na ‘Yan Sandan Najeriya

8. Babban Daraktan Hukumar Tsaro ta NIA

9. Babban Daraktan Hukumar Tsaro ta Farin Kaya, DSS

10. Babban Akawun Kotun Kolin Najeriya

11. Wakilai biyu da zababben Shugaban Kasa zai nada

Sakataren Gwamnatin Tarayya ne zai kaddamar da wannan kwamitin ranar Talata 14 ga watan Fabrairun 2023 da karfe 12 na rana a ofishin Sakataren Gwamantin Tarayya.

Baya ga wannan, Sanarwar ta ce Shugaba Buhari ya sanya hannu kan wata dokar shugaban kasa mai lamba 14 ta 2023 kan Gudarwa da Tafiyar da Ayyukan Kwamitin Mika Mulki na Mukamin Shugaban Kasa.

PRNigeria hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1255 days 4 hours 8 minutes 57 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1237 days 5 hours 50 minutes 22 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com