Shugaba Buhari na jagorantar taron Majalisar Koli ta Kasa domin tattauna batutuwan da ke ci wa Najeriya tuwo a kwarya.
A na sa ran taron Majalisar da ke gudana a Fadar Shugaban Kasa zai tattauna kan matsalar mai, sauyin kudi, karancin takardun Naira da kuma sha’anin tsaro gabanin babban zabe da za a yi nan da mako biyu.
Taron ya samu halartar tsoffin shugabannin kasa irin su, Abdulsalami Abubakar, Goodluck Jonathan, Olusegun Obasanjo, da kuma Yakubu Gowon da gwamnoni da kuma Shugabannin Majalisar Dokoki ta Kasa.
Majalisar Koli ta Kasa wani bangare ne Gwamnatin Najeriya da ke ba da shawarwari kan tsare-tsaren gwamnati a bangaren zartaswa.
Mahalarta zaman na ranar Juma’a sun hada da Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da Shugaban ’Yan Sandan Najeriya.
Haka kuma taron ya sami halartar Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya da sauransu.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1255 days 4 hours 51 minutes 30 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1237 days 6 hours 32 minutes 55 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com