Tsohon Firaministan Sudan Abdallah Hamdok ya yi gargaɗin cewa rashin tsaron da ƙasar ke fuskanta zai iya zarta na Siriya da Libya.
Mista Hamdok na wannan maganar ne yayin da ake ci gaba da samun rahotonnin kai farmaki da jiragen sama a kan wuraren da ke hannun dakarun RSF a birnin Khartoum.
Read Also:
Duk ɓangarori biyun da ke yaƙi da juna na zargin juna da karya yarjejeniyar tsagaita wuta. Dubban mutane ne suka fice daga gidajensu sakamakon yaƙin.
Tsohon Firamistan ya bayyana yaƙin da rashin hankali tare da cewa yaƙi ne da babu wanda zai yi nasara a cikinsa, sai dai hasarar rayuka masu yawa da zai haifar.
Ya ce akwai buƙatar ƙasashen duniya su yi aiki tare domin zaunar da shugabanin rundunonin da ke yaƙi da juna a ƙasar da jagoran dakarun RSF a teburiun sulhu domin kawo ƙarshen yaƙin.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 21 hours 4 minutes 55 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 22 hours 46 minutes 20 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com