Gwamnatin tarayyar kasar Nijeriya ta kaddamar da wani shiri na horas da ma’aikatanta dubu 10 hanyoyin tattara bayanai na zamani domin gudanar da ayyukan su cikin tsari.
Hukumar dake lura da bayanai ta kasar nan wato Nigeria Data Protection Commission da hadin gwiwar Data.org ne suka shirya gudanar da shirin, domin horas da ma’aikatan gwamnatin tarayyar kasar nan abinda dokar tattara bayyanai ta shekarar 2023 ta kunsa domin sanya su a turbar data dace wajen gudanar da ayyukan su.
Read Also:
Ministan yada labarai, kirkire-kirkire da tattalin arziki na zamani, Dr. Bosun Tijjani yace hadin gwiwa tsakanin hukumar ta NDPC da Data.org kamar wani somin tabi ne cikin a yunkurin hukumar na daidaita ayyukan ma’aikatan Gwamnatin tarayya tare da inganta musu shi da ilimi da dabaru.
Wadanda zasu rabauta da wannan horo dai sun hadar da shuwagabanin bayanai, manyan dakarun tattara bayanan tsaro, da kuma da kuma masu lura da tattara bayanai gami da masu kula da tsaron na’ura mai kwakwalwa wanda ke aiki a ma’aikatun gwamnatin tarayya.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1255 days 44 minutes 18 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1237 days 2 hours 25 minutes 43 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com