Adadin mutanen da ambaliya ta kashe a Maiduguri ya kai 30- NEMA

Hukumar bayar da agajin gaggawa a Najeriya NEMA ta fara tattara alƙaluman mutanen da suka rasa rayukansu  bayana aukuwar  ibtila’in ambaliyar ruwan a birnin Maiduguri na jihar Borno dake arewa maso gabashin Nijeriya a cikin daren Talatar da ta gabata.

Mahukuntan jihar sun ce zuwa yanzu an tattara gawarwakin mutane 30 yayin da NEMA ke ci gaba da aikin laluben waɗanda suka maƙale a saman rufin gidaje da wurare masu haɗari.

Hukumar NEMA ta ce ambaliyar ta shafi mutane miliyan 1 da rabi waɗanda ke halin tsananin buƙatar agaji, musamman ganin yadda suka bar muhallansu a yanayi na ɗimuwa sakamakon mummunar ambaliyar wadda ta faro da tsakaddaren Talata.

Kakakin hukumar ta NEMA Ezekiel Manzo ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa kawo yanzu mutane 30 suka tabbatar da mutuwarsu ko da ya ke alƙaluman ka iya ƙaruwa sakamakon yadda har yanzu aka gaza gano mutane da dama da suka bace a ruwan.

Tun farko ɓallewar madatsar ruwa ta Alau ita ta haddasa tumbatsar ruwa a tituna da magudanan Maiduguri wanda zuwa yanzu ya lalata tarin kadarorin da ba a kai ga ƙiyasin ƙudinsu ba, baya ga ginaku da gidajen jama’a da kuma wuraren kasuwanci.

PRNigeria hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 15 hours 28 minutes 56 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 17 hours 10 minutes 21 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com