Shugaban sojin Burkina Faso ya ce yana shirin ƙwace lasisin haƙar ma’adinai da aka bai wa kamfanonin ƙasashen waje domin bayar da su ga ƙungiyoyin haƙar ma’adinai na cikin ƙasar.
Captain Ibrahim Traore ya bayyana haka ne cikin wata hira da wani gidan radiyon ƙasar kan cikar juyin mulkin – da ya kai shi kan karagar mulkin ƙasar – shekara biyu.
Shugaban dai bai bayyana sunayen kamfanonin da zai ƙwace wa lasisin ba.
Read Also:
Kamfanonin haƙar ma’adinai na ƙasashen Australian da Birtaniya da Canada da kuma Rasha na daga cikin kamfanonin da yanzu haka ke aikin haƙar ma’adinin zinare a Burkina Faso.
Matakin na zuwa ne bayan makamancinsa a ƙasashen Mali na Jamhuriyar Nijar, waɗanda dukansu yanzu ke ƙarƙashin mulkin sojoji.
A duka ƙasashen uku an samun ƙaruwar ayyukan masu iƙirarin jihadi, lamarin da ya raba miliyoyin mutane da muhallansu, yake kuma barazana ga ayyukan haƙar ma’adinai.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 7 hours 36 minutes 50 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 9 hours 18 minutes 15 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com