Home SIYASA APC ta Mutu, Allah ya ji Kanta – Dino Melaye

APC ta Mutu, Allah ya ji Kanta – Dino Melaye

Lagos
Akinwunmi-Ambode lagos Governor

APC ta Mutu, Allah ya ji Kanta – Dino Melaye

 

A yanzu haka, rikicin shugabanci ya baibaye jam’iyyar APC gabannin babban taronta na kasa.

Sanata Dino Melaye ya yi amfani da wannan damar wajen yi mata ba’a, inda ya ce an yi juyin mulki a jam’iyyar mai mulki.

Ya kuma sanar a shafinsa na soshiyal midiya cewa APC ta mutu tare da yi mata addu’an samun rahama

Gabannin babban taron jam’iyyar All Progressives Congress (APC) wanda za a yi a ranar 26 ga watan Maris, sabon rikicin shugabanci ya kunno kai a jam’iyyar mai mulki.

Hakan ya biyo bayan darewa kujerar Gwamna Mai Mala Buni da Gwamna Sani Bello na jihar Neja ya yi a matsayin shugaban riko na jam’iyyar ta kasa, a ranar Litinin, 7 ga watan Maris.

Wannan ya sa Sanata Dino Melaye, tsohon dan majalisa da ya wakilci Kogi ta yamma a majalisar dattawa, yiwa jam’iyyar mai mulki ba’a.

An yi juyin mulki a APC – Dino Melaye

Dino ya je shafinsa na Instagram inda ya yi wani rubutu kan rikicin na APC sannan ya ce an yi juyin mulki a jam’iyyar mai mulki.

Ya ce: “Kwace ya kwace daga hannun wanda ya kwace….yepaaaaa. Juyin mulki a APC.”

APC ta mutu, Allah ya ji kanta

Dan siyasar bai tsaya a nan ba, ya kuma wallafa cewa APC ta mutu tare da yi mata addu’an Allah ya ji kanta.

Ya rubuta a shafin nasa:

“RIP APC: 2014 – 2022. Shekaru 8. Kin tafi da wuri haka. Mai sanarwa – SDM”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp