Kotu ta Bawa Jam’iyyar APC Ranar da Zata Gudanar da Babban Taronta na Kasa
Wata babbar kotu a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya ta yanke hukuncin kyale jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta gudanar da babban taronta na kasa a ranar 26 ga watan Maris na wannan shekarar.
A ranar Juma’a alkalin kotun, Mai shari’a Bello kawu ya yanke hukunci cewa ‘ya’yan jam’iyyar ba su da hurumin kai kararta.
Ya ce wani umarnin Kotun Kolin Najeriya kan wani batu irin wannan ya sha gaban wanda babbar kotun ta fitar na 18 ga watan Nuwambar bara.
Kotun ta daga zamanta zuwa ranar 30 ga wannan watan na Maris domin ci gaba da sauraren karar.
Wani mamba a jam’iyyar mai suna Salisu Umoru ne ya shigar da kara inda yake so kotun ta hana jam’iyyar ta APC da gwamna Mai Mala Buni da kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya, INEC su shirya babban taro na kasa na jam’iyyar har sai bayan an kammala sauraren karar da ya shigar.
Yadda matsalar ta samo asali
Yayin da damuwa ke karuwa tsakanin manyan jami’an jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, wata kotu za ta yanke hukunci kan karar da aka shigar a gabanta wadda ake neman a soke wani umarni da ya hana jam’iyyar gudanar da babban taronta na kasa ranar 26 ga watan Maris.
Cikin mako biyun da suka gabata wasu gwamnonin jihohin kasar sun yi kokarin sauya shugabannin jam’iyyar, matakin da ya janyo karuwar fargaba da matsaloli ga ‘ya’yan jam’iyyar.
Read Also:
Sau uku ana cin karo da matsaloli yayin da ‘ya’yan jam’iyyar ke kokarin samar da shugabanin da za su karbi ragamar jam’iyyar daga hannun kwamitin riko karkashin gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni.
Karar da aka shigar a gaban kotun wanda ke son a kawar da umarnin kotun na ranar 18 ga watan Nuwamba 2021 ya gamu da cikas bayan da wasu lauyoyi biyu, Shuaibu Aruwan (SAN) da Michael Adoyi suka sanar da kotun cewa sune ke wakiltar jam’iyyar.
Bayan da kotun ta zauna ranar Talatar da ta gabata, Mista Aruwan ya sanar da kotun cewa ya sami wata wasika daga jam’iyyar APC da ta tabbatar da nadinsa a matsayin lauyan jam’iyyar a wannan shari’ar kamar yadda kotun ta umarci a yi.
Daga nan sai ya nemi kotun ta kawar da umarnin kotun na farko saboda rashin hurumi.
Amma lauya Mike Enahoro-Eba, wanda shi ke wakiltar wadanda suka shigar da karar ya ki amincewa da wannan bukatar, yana cewa dokokin kotun sun bukaci a bayar da kwanaki bakwai domin wadanda ake kalubalanta su sami damar mayar da martani.
Daga nan ne alkalin da ke sauraron karar, Mai shari’a Bello Kawu ya ajiye ranar Juma’a 18 ga watan Maris domin yanke hukunci.
Ganin muhimmancin wannan ranar ga jam’iyyar ta APC, masana siyasar Najeriya na cewa rashin warware wannan matsalar na iya haifar da babban kalubale ga jam’iyyar ta APC mai mulkin Najeriya ganin cewa kasa da shekara guda ya rage a gudanar da babban zabe a kasar, wanda ‘yan kasar za su zabi sabon shugaban kasa da gwamnonin yawancin jihohi da kuma ‘yan majalisun tarayya da jihohin kasar.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 14 hours 57 minutes 50 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 39 minutes 15 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com