Na Janye Daga Neman Takarar Shugbancin Jam’iyyar APC – Ali Modu Sheriff
Tsohon gwamnan Borno da ke arewa maso gabas, Ali Modu Sheriff, ya ce ya janye daga takarar neman shugbancin jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya.
Modu Sheriff ya faɗa wa BBC Hausa cewa ya janye takarar ce saboda biyayya ga Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.
“Shugaban ƙasa na son shugaban jam’iyya ya fito daga Arewa ta Tsakiya. Shugabanmu ne, babanmu ne, duk abin da yake so shi za mu yi. Ni ba na jayayya da iyayena a kowane fanni,” in ji shi.
Matakin tsohon gwamnan na zuwa ne bayan jam’iyyar ta ce ta ware wa shiyyar arewa ta tsakiya muƙamin shugaba na ƙasa yayin ganawar da gwamnoninta suka yi da Shugaba Buhari a watan Fabarairu.
Read Also:
An ware wa shiyyoyin Arewa muƙaman da na Kudu suka riƙe a cikin shekara takwas da suka wuce, su ma na Kudu haka, a cewar Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai.
Bisa wannan tsari ne jam’iyyar za ta zaɓi ssabbin shugabanninta a babban taron da za ta gudanar ranar 26 ga watan Maris.
‘Matakin da zan ɗauka nan gaba’
Ali Modu Sharif ya gode wa dukkan mutanen da suka goya masa baya”, amma ya ce ba zai daina siyasa ba.
“Ina jira daga nan zuwa Juma’a, idan jam’iyya ta ce kowane yanki zai iya tsayawa takara ina nan,” a cewarsa.
Da aka tambaye shi ko zai bar siyasa, sai ya amsa da cewa: “Ba zan bar siyasa ba. Don me zan bar siyasa?
“Ba zan nemi wani muƙami ba sai na shugaban jam’iyya saboda na taimaka wa jam’iyyarmu mai girma.”
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 14 hours 35 minutes 29 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 16 hours 16 minutes 54 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com