Kungiyar YBN ta kaddamar da Karin Reshe Uku a Tafiyar ta
Kungiyar tallata takarar shugabancin kasa ta Gwamna Yahaya Bello,wato Yahaya Bello Network (YBN) sun kaddamar da karin reshina guda 3 a karkashin kungiyar,wannan na zama karin azamar zurfafa kyakkyawar manufar tafiyar domin ganin hakar cimma ruwa bisa manufar siyaya a doron jagorancin Gwamna Yahaya Adoza Bello domin karbar Jagorancin kasar nan.
Kungiyar ta YBN tana kunshe da reshina guda bakwai mabambamta,Wanda kaddamar da guda uku a yanzu,jumullar su yazama guda goma.
Reshinan da aka kaddamar sun hada da reshen dalibai, da reshen mutane masu bukata ta musamman da Kuma ‘yan siyaya tun daga tushe.
A jawabin maraba daga bakin shugaban kungiyar Alhaji Abdurahman Muhammad Maikwashewa ya bayyana cewar manufar kungiyar ta YBN shine aiki tukuru wajen ganin Gwamna Yahaya Bello ya cimma muradansa a siyasace domin ganin cigaban kasa Nigeria, habbaka tattalin arziki,samar da ingantaccen tsaro, nagartaccen ilimi, kyakkyawan yanayi a harkar lafiya,dabbaka da’a da kuma tarbiyya.
Read Also:
Gwamna Yahaya Bello Wanda yasamu wakilcin shugaban ma’aikata na Jihar Kogi Jami’u Asuku, yayin dayake kaddamar da reshinan ya bayyana jin dadin sa,da gamsuwar sa bisa wannan tsari da kungiyar YBN tayi da zurfin tunani gami da kyakkyawan hange wajen zakulo wadannan sahun mutane a cikin al’umma domin bada gudunmuwa a cikin tafiyar.
Dayake zantawa da ‘yan Jarida Shugaban na YBN Maikwashewa ya bayyana cewar kaddamar da wannan Rassa na da nasaba da la’akari da muhimmancin da dalibai suke dashi wajen samar da kasa Abar alfahari,kazalika masu bukata ta musamman na da gudunmuwa mai yawa da zasu iya bayarwa a al’umma,a matsayin su na ‘yan kasa jawo su jiki a dama dasu a harkoki da fannoni da dama na rayuwa na da tasiri kwarai.
Daga nasu bangaren reshinan da aka kaddamar sun bayyana tsagwaron farin cikin su,kana sun bayyana cewar sun nemi su bada gudunmuwa a tafiyar ne,sabili da bayan hange mai nisa sun tuke magaryar aminta cewar Gwamna Yahaya Bello shine mafita ga matsalolin kasar nan.
Kwamishinoni da kusoshin gwamnati daga Jihar Kogi sun samu halartar taron tare manyan taurarin masana’antar shirya shirya fina finai ta Kannywood, ‘yan jarida da dubban mutane.
Daga cikin jihohin da aka kaddamar da reshinan sun hadar da Jihar Kano,Jigawa, Nassarawa,Sokoto,Yobe,Gombe,Kwara,Adamawa,Filato,Zamfara,Borno,Katsina,Benue, Abuja,Kebbi,Kogi da Kuma Taraba.
Matashin ‘Dan Jarida
Musa Sani Aliyu
24-03-2022
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 14 hours 4 minutes 47 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 15 hours 46 minutes 12 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com