Home SIYASA Shugaba Buhari ya ta ya Tinubu Murnar Cika Shekaru 70 da Haihuwa

Shugaba Buhari ya ta ya Tinubu Murnar Cika Shekaru 70 da Haihuwa

Shugaba Buhari ya ta ya Tinubu Murnar Cika Shekaru 70 da Haihuwa

 

Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, jigon jam’iyyar APC kuma dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, zai cika shekaru 70 a ranar Talata, 29 ga Maris.

Gabanin bikin zagayowar ranar haihuwarsa, shugaba Buhari Buhari ya fitar da sanarwar taya murna ga tsohon gwamnan jihar Legas.

Shugaban ya jinjinawa jajircewa, juriya, rashin nuna son kai da martabar Tinubu wajen fifita jin dadin al’umma da hadin kan al’umma sama da son rai.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bi sahun ‘ya’yan APC da shuwagabanninta wajen taya jagoran jam’iyyar na kasa kuma tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu murnar cika shekaru 70 da haihuwa a ranar 29 ga Maris, 2022.

Shugaban kasar, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin ta hannun mai magana da yawunsa, Femi Adesina, ya tabbatar da irin gudunmawar da jigon na APC ke bayarwa ga ci gaban siyasa, tattalin arziki da zamantakewar kasar nan.

Daily Trust ta rahoto cewa, Buhari ya kuma yaba da jajircewarsa, juriyarsa, rashin nuna son kai da martabarsa a ko da yaushe yana fifita hadin kan al’umma sama da son kai.

Hakazalika, tare da samun goyon baya da hangen nesan Najeriya mai girma ta hanyar zuba jari ga mutane, hukumomi da gwamnatoci, ba tare da tunanin kabilanci ko akida ba.

Ya kuma yi addu’ar Allah ya karawa Asiwaju Tinubu, Jagaban Masarautar Borgu karfi da lafiya da hikima domin ya ci gaba da yi wa kasa hidima da kuma bil’adama baki daya.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp