Yanzu – Yanzu: Dattawan Arewa Sun Bukaci Buhari yayi Murabus

Kungiyar Dattawan Arewancin Nijeriya ta bukaci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sauka daga shugabancin Kasar, sakamakon kashe-kashen rayuka dake faruwa a fadin kasar, musamman Arewaci.

Daraktan Yada Labarai da  Shawarwari na Kungiyar Dr. Hakeem Baba-Ahmed ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.

“Gwamnatin Shugaban Muhammadu Buhari bata da abinda zata ce mana a fannin tsaro, sakamakon kalubalen da muke fuskata. baza mu iya cigaba da zama karkashin umarnin masu kashe mutane, Garkuwa, Fyade da dukkannin kungiyoyin dake tauye hikkin mu na rayuwa, kuma su kasance cikin kwanciyar hankali da nutsuwa ba, duk da irin wadannan muggan ayyukan da suke aikatawa.

“Kundin Tsarin Mulkin mu ya tanadi cewa Shugabanni suyi Murabus bisa radin kansu, idan aka kalubalance su da wasu dalilai, ko kuma suka gaza a harkokin shugabanci.

Sanarwar ta ce,”yanzu lokaci ya yi da Shugaba Buhari zai yi la’aka da wannan zabi. Tun da shugabancinsa ya gaza iya samar da inganataccem tsaro ga ‘yan Nijeriya. Kungiyar mu na sane da wannan shawara, kuma ba za mu ci gaba da rayuwa a cikin  wannan yanayi ba har sai shekarar 2023 lokacin da wa’adin shugaban Buharin zai kare.

Kungiyar ta kuma ce ta bayar da wannan shawara ne la’akari da nauyin daya rataya a wuyansa, sannan kuma ta bukaci wadanda yake jin maganar su dasu bashi shawarar ya yi murabus.

Ta cikin sanarwa kungiyar ta bayyana bakin cikin ta kan abinda ta kira kashe-kashen gami da cin zarafin Al’umma ya zama tamkar Ruwan dare, yanzu yin Balaguto ga ‘Yan Nijeriya ya zama hadari, kuma idan mutum ya zauna a gida ma bai tsira ba.

Ta cikin sanarwar kungiyar ta bukaci dukkannin masu zawarcin kujerar shugaban kasa a kakar zaben 2023, da suyi karatun ta Nutsa, su lura da kalubalen shugabanci dake gaban su da idon basira.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 14 hours 47 minutes 8 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 16 hours 28 minutes 33 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com