Babban Sifeto Janar na ‘Yan sandan Najeriya IGP Usman Alkali Baba, ya daga likafar kananan Jami’an Rundunar ‘Yan Sandan Kasar kimanin 21,039 a ranar Laraba.

Wannan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Mukaddashi Kakakin Hukumar na kasa CSP Olumuyiwa Adejobi wadda aka raba ga menema labarai a Birnin Tarayya Abuja .

Sanarwar tace an daga likafar Kananan Jami’an ne, wanda suka sami Karin matsayintu kafin ko a tsakanin shekarar 2017.

Karin matsayin da ya kunshi Sajan guda 20,572 wanda aka kara musu matsayi zuwa Safeto, sai masu mukamin Kofur su 324 wanda aka kara musu matsayin zuwa Sajan.

Sanarwar tace wannan wani bangare ne na kokarin da hukumar ke yi na inganta Jin dadi da walwalar Jami’an Rundunar ta ‘Yan Sanda, tare da samun Karin karfin gwuiwar gudanar da ayyukan su yadda ya kamata.

Alkali Baba yace yin Karin girma ga jami’an  na daga cikin kudirce-kudircensa na bunkasa Hukumar domin tabbatar da cewa anyi Karin ga wadanda suka cancanta, don kara kwazo da sadaukarwa yayin da suke gudanar da ayyukan su.

Daga bisani Sifeto Janar na ‘Yan Sandan yayi bukaci jami’an da suka sami Karin girma dasu kara jajircewa, su kuma kara zage damtse, tare da sanya ksihin kasa a yayin da suke gudanar da ayyukan su.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1190 days 4 hours 38 minutes 57 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1172 days 6 hours 20 minutes 22 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com