Wani harin ‘Yan Bindiga yayi sanadiyyar halaka akalla mutun 4 a garin Ayilamo dake Karamar Hukumar Logo ta Jihar Benue.
Mazauna garin sun shaidawa PRNigeria cewa lamarin ya auku ne tsakar daren Talata yayin da al’ummar yankin ke tsaka da bacci.
Read Also:
Inda ‘Yan bindigar suka yiwa garin tsinke, tare da tsallakawa gidajen Al’umma inda suka harbe mutum 4 tare da barin wasu cikin muggana raunika.
Guda cikin shuwagabannin al’ummar garin, ya bayyana sunayen wadanda harin ya rutsa dasu da suka hadar da Vaachia Hangeior, Abako Kpeibee, Mtomga Akpi and David Akave.
Kawo lokacin kammala wannan rahoton kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar S.P Catherine Anene bata dauki kiran da muka yi mata ba, kuma bata bada amsar sakon karta kwana da muka tura mata ba.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1486 days 1 hour 17 minutes 6 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1468 days 2 hours 58 minutes 31 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com