Dakarun sojin hadin gwuiwa na Kasa da Kasa MNJTF sun fatattaki mayakan kungiyar Boko Haram Tsagin ISWAP a yankin tafkin Chadi.
Wata majiya ta shaidawa PRNigeria cewa sojojin sun kai farmaki kan maboyar ‘yan Ta’addan dake kauyen Ndaurori, wani gani mai iyaka da Nijeriya da Jamhuriyya Nijar.
Read Also:
A yayin harin an halaka ‘yan bindigar da dama, inda wasu suka tsere cikin daji da tabon harbi a jikkunan su, an hangi baburan hawa da gawarwakin ‘yan bindigar a barbaje a wajen.
Majiyar ta tabbatar da cewa harin ya tilastawa ‘yan bindigar tserewa ta yankin Bulabulin gari mai nisan kilomita 28 da garin Damasak inda suke boye.