‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 6 A Jihohin Kaduna Da Bauchi

Wasu mabanbanta hare-hare sunyi sanadiyyar mutuwar mutum 6 a jihohin Kaduna da Bauchi.

PRNigeria ta ruwaito cewa maharani da ake zrgi ‘yan bindiga ne suna halaka wasu manoma a gonakin su a kauyen Iyatawa dake karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.

‘yan uwan wadanda lamarin ya rutsa dasu sunce mazauna kofar Jatau ne dake garin Zari’a, sun ce ‘yan  uwan nasu sun je gonakin nasu ne domin yin shuka, nan ne ‘yan bindigar suka haike musu, suka kuma halaka mutum 2 tare da yin garkuwa da  mutum 3.

Sun bayyana sunan wadanda ‘yan bindigar suka halaka da Alh. Mustapha lawan da Bello Lawal.

Sai dai an bayyana cewa ko a daminar Badi mahaifin wadanda aka halaka Alh. Lawal kofar Jatau ya tsallake rijiya da baya tare jin wasu muggana raunika a hannu ‘yan bindigar bayan da yaje gewaya gonar.

A wani labarin kuma wasu da ake zargin ‘yan bindiga sun kai hari garin Jamari Sabuwa dake  karamar hukumar Alkaleri ta jihar Bauchi, inda suka halaka mutum 4 tare da raunata mutum 3.

Shugaban karamar hukumar Alkaleri, Yusuf Garba, ya tabbatar da faruwar lamarin ranar Juma’a a garin Bauchi.

Yace ‘yan bindigar sun shiga garin ne inda sukayi garkuwa da Mai garin garin, bayan da Al’umma suka fahimci abinda ke faruwa ne suka tashi balli tare datarwatsa Shirin ‘yan bindiigar.

Shugaban karamar hukumarya tabbatar da cewa ‘yan bindigar sun fito daga cikin dajjin da yayi iyaka da jihohin Taraba, Gombe da kuma Plateau.

Wakilin mu ya rawaito mana cewa al’ummomin da lamarin ya shafa sun hadar da Tudun wada, Jada, Old Jamari, Sabuwa, Garin, Jauro Bano.

Wani mazaunin yankin Muhammad Usman ya shaidawa wakilin namu cewa ‘yan bindigar sun shiga garin ne da misalin karfe 11:45 na daren ranar Alhamis.

Kawo yanzu dai jami’an ‘yan sandan basu yi cikakken bayani kan wannan lamari ba, amma kakakin rundunar Muhammad Ahmad wakil yayi alkawarin tuntubar wakilin mu nan gaba kadan.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 15 hours 10 minutes 16 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 51 minutes 41 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com