Dakarun Soji Sun Hallaka Jagoran ‘Yan Ta’adda ‘Shanono’ A Jihar Kaduna, Da kuma wasu Mayakan Boko Haram A Jihar Borno.

Sojoji sun sami nasarar hallaka guda cikin Gaggan ‘yan ta’adda, gami da ‘yan ta’addan masu tarin yawa a yayin wani  harin da dakarun sojin saman Nijeriya suka kai kan mayakan.

da Mayakan kungiyar ta boko haram tsagin ISWAP.

Sojojin sun halaka da dama cikin ‘yan kungiyar ta boko haram a cikin wani kazamin hari ta sama da jiragen sojojin Nijeriya biyu suka kai,  yayin da mayakan kungiyar boko haram ke gwabza fada a yankin Arewa maso gabashi.

a wani hari kuma rundunar ta sami nasarar hallaka jagoran ‘yan ta’addan dake gudanar da ayyukan ta’addancin sa a jihar Kaduna, wanda aka fi sani da Alhaji Shanono, wanda Harbin bindiga ya hallaka yayin harin na sojin sama.

Wata majiyar tsao ta tabbatar da cewa, rundunar sojin ta sami wannan nasarar ne yayin da mayakan na bokon haram tsagin Abubakar shekau ke gabza fada tsakanin su da mayakan kungiyar tsagin ISWAP a jihar Borno.

Ko da yake PRNigeria bata tabbatar da Adadin mayakan kungiyar boko haram nawa aka hallaka ba, amma ta sami labarin cewa rundunar sojin Nijeriya ta kai hari kan mayakana garin Gazuwa mai tazara kilomita 1.2 da garin Gargash.

Wata majiya daga rundunar Sojin Nijeriya da ta bukaci a sakaye sunan ta bayyyna cewa runanin da bangarorin biyu suka shiga ya bada damar musu harin ba-zata da jiragen yakin na soji.

Haa kuma PRNigeria ta tattara cewa biyo bayan wani bayanin sirri ai dauke da kwanan watan 9 ga watan Agustan 2022, Shanono na shrin gudanar da wani taron ganwa da mayakan dake biyayya ga dabar sa a kauyen Ukambo mai nisan kilomita 131 daga jihar Kaduna, don haka ne dakarun Operation Whirl Punch suka baza koma a yankin domin gudanar da aikin daya kamata.

By PRNigeria

 

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 15 hours 4 minutes 38 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 46 minutes 3 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com