Dakarun soji sun sami nasarar kubutar da mutum uku a hanyar zaria zuwa kano yayin da suke gudanar da sintiri a Ungwan Namama.
Wannan dai na cikin wata sanarwa da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gid ana jihar kaduna Samuel Aruwan ya fitar, wadda ta ambaci sunan mutum Uku da suka hadar da Abdullahi lawal, sadiya Salimanu da kuma karamar yarinya mai kimanin watannin 10 a duniya.
Read Also:
Sanarwa tace dakarun sojin sun yi arangama da ‘yan ta’addan da a yankin inda bayan arangamar suka tsere suka bar mutum ukun da suka yi garkuwar da su.
Wani bincike ya tabbatar da cewa wadanda aka tseratar din ‘yan ta’addan sun yi garkuwa dasu ne a wani gari dake mokataka da garin.
Haka kuma yayin artabun dakarun sojin sun sami nasarar kwato dabbobi 9 da suka hadar da Saniya guda daya da tumaki takwas.
Daga bisani gwamnatin jihar kaduna ta jinjinawa dakarun sojin bisa namijin kokarin da sukayi na kubutar da wadanda akayi garkuwar da su.
PRNigeria
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1485 days 20 hours 31 minutes 53 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1467 days 22 hours 13 minutes 18 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com