Majalisar Dinkin Duniya ta kada kuri’ar yin tir da Rasha kan mamaye wasu sassan Ukraine da ta yi, matakin da shugaban Amurka Joe Biden ya ce sako ne mai karfi ga takwaransa Vladmir Putin.
Read Also:
Kasashe 143 ne suka goyi bayan kudurin na yin tir da Rasha a zauren Majalisar Dinkin Duniyar, inda 5 suka hau kujerar naki, sauran kasashe 35 kuma suka kauracewa zaman, wadanda suka hada da China, India, Afirka ta Kudu da kuma Pakistan, duk da matsin lambar da Amurka ta rika musu kan su yi tir da Rashan; kamar yadda jaridar Reuters ta ruwaito.
Kudurin dai ya yi tir da matakin Rasha, na shirya zaben raba gardama a cikin iyakokin Ukraine” da kuma “yunkurin mamaye yankuna hudu na kasar ta karfin tsiya da shugaba Vladimir Putin ya sanar a watan jiya.
Ko a watan Satumban da ya gabata, sai da Majalisar ta nufaci kada makamanciyar kuri’ar amma Rasha ta yi amfani da kujerarta wajen dakile yunkurin duk da matakin Amurka na kafiya don tabbatar da ganin an yi tir da Moscow.
PRNigeria
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 12 hours 16 minutes 39 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 13 hours 58 minutes 4 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com