Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa Nijeriya na fatan yin aiki tare da sabon firaministan Burtaniya Rishi Sunak, a banagarori da dama da suka hadar da yaki da ta’addanci, samar da abinci gami da makamashi da tunkarara matsalar sauyin yanayi.
Wannan na kunshe ne ta cikin wata takardar sanarwa da kakakin shugaban kasa Garba shehu ya fitar, mai taken kalaman shugaba muhammadu Buhari kan firamininsta burtaniya mai jiran gado, Rt Hon. Rishi Sunak MP.
Read Also:
Sanarwar take madadin gwamnatin tarayyar Nijeriya, dake matsayin babbar kasa cikin kasashe 21 na Nahiyar Afirka dake kkungiyar kasashe rainon Ingila ta commonwealth na yiwa Rishi Sunak maraba da shiga Ofishi.
“Matsayinsa na firaminista na farko daga jini biyu wato burtaniya da Asiya kuma mafi kankata a cikin shekaru 200, wannan zai kasance wani abin laka’akai ga matasa a cikin al’ummar mu biliyan 2.4 a kasashe 56 na Commonwealth”.
“A wannan muhimmayar rana, yana da kyau mu tuna da kyakkyawar alakar dake tsakanin kasashen mu Burtaniya da Nijeriya”.
Shugaban ya kara da cewa kungiyar kasashe renon ingila za ta tsaya tsayin daka wajen yakar ta’addanci tare da sabunta kudirorin ta na magance matsalar karancin abinci a duniya da ke haddasa tsadar rayuwa ga Al’ummomin duniya baki daya.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 12 hours 14 minutes 43 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 13 hours 56 minutes 8 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com