EFCC ta yabawa CBN bisa Matakin Sauya Fasalin Wasu Takardun Kudin Nijeriya.

Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta yabawa babban banki na kasa bisa matakin sake fasalin wasu  takardun kudin kasar.

Yabon na kunshe ne cikin wata sanarwa da  mai Magana da yawun hukumar Wilson Uwajaren ya fitar bayan taron manema labarai a ranar Laraba a birnin Abuja.

Da yake bayani kan matakin, shugaban hukumar EFCC AbdulRasheed Bawa, yace  matakin ya zo daidai lokacin da ake bukata, mussaman duba da kalubalen da  ake fuskanta ta bangaren kudi, wanda yace ya haifar da koma baya  ga tsare-tsaren hada-hadar kudade

Haka kuma ya bukaci bngaren hada-hadar kudi da cibiyoyin musayar kudaden ketare da su yi aiki bisa sharuddan da  babban bankin ya gindaya, na ganin an janye tsaffin takardar kudi, yana mai gargadin cewa hukumar ta EFCC za ta sa ido na ganin baragurbi basu kawo cikas ga ci gaban ba.

Tare da kira ga bankuna da su yi watsi da duk wani  kokari da za a yi amfani da sun a ganin ba a cimma nasara ga Shirin ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com