Gwamnan Jihar Benuwai, Samuel Ortom Yace Bazai Zabi Bafullatani ba.

Gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom, yace ba zai mara wa ɗan takarar PDP, Atiku Abubakar baya ba a zaben shekarar 2023.

Gwamnan, wanda ya fito daga arewacin Najeriya yace ya gwammaci ya mutu da ya goyi bayan Bafullatani ya zama shugaban ƙasa.

Ortom na ɗaya daga cikin tawagar gwamnoni 5 da suka ware kansu a PDP kuma suka nemi Ayu ya yi murabus.

An ruwaito Gwamnna Ortom na faɗa wa Atiku cewa can ta matse masa, amma ba zai mara masa baya ba yayin da Fulani ke kashe mutanensa a Benuwai.

Ortom ya yi wannan furucin ne ranar Lahadi da daddare yayin da ya karɓi bakuncin gwamnonin 5 G-5 da suka haɗa da, Nyesom Wike na Ribas, Okezie Ikpeazu na Abiya; Seyi Makinde na Oyo da Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu.

Gwamnan ya koka da kisan da aka yi wa mutane 18 a ƙaramar hukumar da ya fito a makon da ya gabata,

“Can ta matse wa Atiku da duk masu goyon bayansa, ku je ku gaya masa shin yana son na zama bawan Fulani ne? Gara na mutu, duk mai ƙaunar Atiku maƙiyin jihar Benuwai ne.” “Ana ta kashe mutane na amma ku ce in yi shiru”.

Wa’adin mulkina zai kare a watan Mayu, daga nan zaku iya mun duk abinda kuka ga dama idan kuna tunanin kuna da mulki, na riga na rubuta wasiyyata.”

“Lokacin da na baiwa matata wasiyyata, shafe dare ta yi tana kuka. Idan na mutu a 62 da yawan sa’annina sun riga ni tafiya. Idan yanzun na mutu na cimma nasara amma kowa ya sani na mutu ne a kokarin kare rayuwar mutane na.”

Ba zan taba goyon bayan Bafillatani ya zama shugaban kasa ba – Ortom Bugu da ƙari, Gwamna Ortom.yace ba zai taɓa tallafa wa Fulani da ɗare kujerar shugaban ƙasa ba a Najeriya.”

“Ba zan taɓa goyon bayan Bafillatani ya zama shugaban ƙasa ba, idan akwai wani mutum da ke bukatar aiki da ni da tabbatar da tsare rayukan mutanena, an shirya aiki da shi.”

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 14 hours 32 minutes 3 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 13 minutes 28 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com