Cif Charles Udeogaranya ya Gargadi ‘Yan Nijeriya Kan Zaben Atiku ko Tinubu

Cif Charles Udeogaranya, ya ja hankalin Al’ummar Nijeriya kan babban zaben kasar dake kara karatowa, inda yace kada su sake suyi uskerin yin zaben tumun dare a kakakar zaben 2023 mai karatowa

Udeogaranya wanda guda ne cikin tsuffin jiga-jigai a jam’iyya mai mulkin kasar ta APC  ya yiwa al’ummar kasar albishir da shan bakar wahala da shiga kangin talauci idan har suka ki zaban Peter Obi na jam’iyyar LP a matsayin shugaban kasa a zabe mai zuwa.

Tsohon jigon na APC ya shawarci ‘yan Najeriya da su kauracewa Bola Tinubu da Atiku Abubakar a 2023 idan har suna son kansu da arziki.

Cif Charles wanda tsohon dan takarar shugaban kasar ne a zaben 2019, ya shawarci ‘yan Najeriya game da wanda ya kamata su zaba a matsayin wanda zai gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari a babban zabe mai zuwa.

Udeogaranya ya gargadi ‘yan Najeriya a kan su shirya shan bakar wahala da tabarbarewar tattalin arziki idan suka ki zaban dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi a 2023.

Gargadin tsohon jigon na jam’iyyar APC na zuwa ne sa’o’i 74 bayan hukumar kididdiga ta kasa ta bayyana cewa ‘yan Najeriya miliyan 133 ne fama da talauci, lamarin da ya dare hasashen bankin duniya kan Najeriya.

A wani jawabi da ya saki a Abuja a ranar Lahadi, dan siyasar ya gargadi yan Najeriya masu zabe wadanda basa daukar batun zaban ingantaccen shugaba muhimmanci da su zauna su sake tunani game da bakar wahala da talaucin mutuwa da zai dabaibayekasar.

Idan yan Najeriya sun san abun da ya fi masu to su kauracewa APC da PDP a 2023

Tsohon mai neman takarar shugaban kasar ya bukaci yan Najeriya da su kauracewa yan takarar shugaban kasa na jam’iyyun All Progressives Congress (APC) da Peoples Democratic Party (PDP).

A cewarsa duk kanwar j ace kuma yakamata mutanen da suka wuce lokacinsu su ba da damar da Najeriya zata rayu idan har suna nufin kasar da alkhairi.

Dan siyasan ya kare kalaman sa  da cewa:

“Idan bamu wuce yan takarar shugaban kasa na APC da PDP ba, za su wuce da kaso 99.9 dinmu zuwa kangin talauci da bakar wahala.”

Muna bayan Peter Obi a 2023 don zagayen Inyamurai ne, Ohanaeze

Jaridar Punch ta rahoto cewa, a bangaren kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta ayyana goyon bayanta ga takarar shugabancin Peter Obi a zaben 2023.

A cewar babban kungiyar mai kare muradan Inyamurai yanzu zagayen kudu maso gabas ne ya samar da shugaban kasar Najeriya na gaba.

 

 

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 15 hours 9 minutes 6 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 16 hours 50 minutes 31 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com