Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewar ana karkatar da wasu makaman da ake amfani da su a yakin dake gudana tsakanin Rasha da Ukraine zuwa Yankin Tafkin Chadi.
Buhari yace ya zama wajibi shugabannin dake yankin su tashi tsaye wajen daukar matakan da suka dace na dakile safarar kanana da manyan makaman dake kwarara zuwa yankin.
Shugaban yace babu tantama yakin Rasha da Ukraine tare da wasu tashe tashen hankulan dake ake fama da su a yankin Sahel sun taimaka wajen rura wutar rikicin Boko Haram a Tafkin Chadi.
Buhari yace duk da yake kasashen dake yankin sun yi kokari wajen dakile kaifin book haram da wasu kungiyoyi makamanta ta a yankin, har yanzu ana fuskantar barazanar yan ta’adda.
Read Also:
Shugaban wanda ya yaba da rawar da rundunar hadin kai ta kasashen guda 4 ke takawa wajen murkushe mayakan boko haram, ya bukace sojojin da su kara kaimi wajen fadada nasarorin da suke samu na kawar da duk wata barazanar da kasashen yankin ke fuskanta.
Buhari ya kuma bukaci kasashen Tafkin Chadin da su tashi tsaye wajen gudanar da ayyukan raya kasa wadanda zasu inganta rayuwar jama’ar su da kuma kare lafiyarsu.
Saboda haka shugaban ya bukaci aiwatar da shirin gina yankunan da aka kwato daga hannun mayakan book haram cikin gaggawa tare da samar da tsaro da kuma kayan more rayuwa.
Babban Sakataren dake kula da Hukumar Tafkin Chadi Ambasada Mamman Nuhu yace Najeriya ta bada kudin da ya zarce Dala miliyan 209 domin gudanar da ayyukan rundunar sojin hadin kan daga shekarar 2015 zuwa 2021.
Shugabannin da suka halarci taron sun hada da shugaban Nijar Bazoum Mohammed da shugaban Chadi Mahamat Idriss Deby da shugaban Benin Patrice Tallon da shugaban Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Fautin Archange Touadera da shugaban majalisar rikon kwaryar Libya Mohammed al Menfi.
PRNigeria
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 14 hours 55 minutes 37 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 16 hours 37 minutes 2 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com