Kwalejin horas da jami’an ‘yan sanda ta Maiduguri ta yayi jami’ai 1180

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya a ranar 29 ga watan Disamba 2022, ta yaye jumullar ‘yan sanda dubu daya da dari daya da tamanin (1180) daha kwalejin ‘yan sanda ta Maiduguri, dake jihar Borno a arewa maso gabashin Nijeriya, ‘yan sandan na cikin wadanda sukayi nasara daga cikin ‘yan sanda dubu goma na shekarar 2021 da suka je atisayen daukar aikin.
Wannan na kushe ta ciki wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ASP Sani Kamilu Shatambaya, a madadin kwamishinan ‘yan sandan jihar Borno; sanarwar tace an gudanar faretin bikin yayi ‘yan sandan a lokaci guda a kwalejojin ‘yan sanda da ke fadin kasar inda aka kamala atisaye na tsawon watannin shida.
A yayin taron yaye ‘yan sanda an gabatar da kyaututtuka ga ‘yan sandan da dama da suka gudanar da abin yabawa.
Da yake jawabi a yayin taron babban sifeton ‘yan sandan Nijeriya Usman alkali baba Psc(+) NPM, fdc NEAPS, CFR wanda ya sami wakilcin mataimakin babban sifeton ‘yan sandan mai lura da sashen ‘yan sanda kwantar da tarzoma AIG ALI JANGA, ya bukaci sabbin ‘yan sanda dasu kasance masu gaskiya da Da’a wannan zai taimaka musu wajen cimma gaci a lokacinda suke gudanar da ayyukan su.
Sifeton janar din ya kuma bayyana cewa, za’a mayar da kananan ‘yan sandan zuwa kananan hukumominsu na asali domin cigaba da sanya dabarun ‘yansan na gwamnatin tarayya na mangace aikata gama-garin laifuka, tare da dakile aikata manyan laifukan a wuraren da aka turasu.
Kwamandan kwalejin DCP Bethrand Onuoha, da yake jawabin rufe taro, ya godewa babban sefeton ‘yan sandan Nijeriya, sannan ya bukaci sabbin ‘yan sanda dasu yi amfani da abinda aka koyar da su.
Kwamishinonin ‘yan sandan jihar Borno, Yobe da kuma Adamawa da kuma wasu manyan jami’an ‘yan sandan Nijeriya sun sami halartar taron yaye jami’an.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 15 hours 34 minutes 55 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 17 hours 16 minutes 20 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com