Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa reshen jihar kaduna ta sami nasara kame wasu da take zargin safarar miyagun kwayoyi dauke da jaka 298 na Cannabis Sativa.
Kwamandan hukumar na jihar Mista Ibrahim Braji ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai ranar laraba a jihar kaduna dake arewa maso yammacin Nijeriya.
Yace jami’an hukumar sun sami nasara kame wadanda ake zargi a yammacin ranar laraba a kauyen tasu mahuta a kan hanyar refinery, dake karamar hukumar chikun.
Yace sun kama wadanda ake zarne ne da suka hadar da maza 2 mata 2 dauke da cannabis mai nauyin kilogram dubu 3,576kg.
Yace ana gudanar da bincike kan lamarin domin gano sauran wadanda ke da hannu a safara, haka kuma rundunar ta sake fadada ayyukanta a jihar domin dakile ayyukan safarar miyagun kwayoyin.
Ya bayyana sabbin rashen hukumar da suka hadar da na makarfi, soba, kaduna North da kuma kaduna South, inda yacean kuma girke matocin sintiri a samara, zaria da sanga.
Braji ya kara da cewa kasancewar zaben 2023 na karatowa, hukumar zata shirya gangamin wayar da kan matasa matsalilin shan miyagun kwayoyi, da kuma matsalar sa agaresu.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 18 hours 31 minutes 51 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 20 hours 13 minutes 16 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com