Mayakan ISWAP Sun mika wuya a Jamhuriyyar Nijar

Mayajan kungiyar tada kayar Baya na ISWAP da suka tsallake rijiya da baya, bayab harin da tsagin Boko Haram ya kai mu a Kayowa da Toumbun Gini, a Arewa maso gabshin yankin Tafkin Chadi, sun mika wuya hannun hukumomi a Tumour, ta Jamhuriyyar Nijar.
Zagazola ya ruwaito cewa mayakan ISWAP sun mika wuya a ranar 10 ga watan Janairu biyo bayan harin da abokan hamayyar su ta boko haram ke kai musu.

Harin ISWAP kan sansanin boko haram ya haifar da asarar rayuka tun a ranakun 31 ga Disamba da kuma 8 ga watan Janairun, 2023.
Harin kungiyar ta kai bisa jagorancin ABU UMAIMAH da akafi sanj da BAKOURA DORO, ya tarwatsa maboyar yan Ta’addan dake Toumbum Allura, Kurnawa, Kayowa da kuma Toumbun Gini, wanda ya tilastawa Abu Moussab al-Barnawi da wasu kwamandojin tsirewa.

Ci gaba da fafatawa tsakanin JAS da ISWAP dai da alama dai ba mai karewa ba ce ganin yadda yunkurin da kungiyoyin ke yi na hada karfi da karfe domin yakar sojojin Najeriya da na MNJTF ya gagara.

Dangane da wannan yanayin ne kungiyar ISWAP ke neman goyon bayan mayakan ISIS na kasashen waje da suka hadar da Mali, Burkina Faso da Somaliya don taimaka musu su karya JAS.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 19 hours 36 minutes 9 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 21 hours 17 minutes 34 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com