An sanya dokar hana fita a Jihar Niger

Gwamnatin jihar Niger ta sanya dokar ta baci biyo bayan kisan wani mai gari a jihar.
Gwamnan jihar Niger Abubakar Sani Bello ya sanay dokar hana zirga-zirga a kauyen
Lambata dake karamar hukumar Gurara, biyo bayan wata hatsaniya da tayi sanadiyyar hallaka wani mai rike da sarautar gargaji Mohammed Abdulsafur.
Wannan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da sakataren Gwamnati jihar Ahmed Matane, ya fitar a ranar lahadi a Minna babban birnin jihar.
Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan daba sun hallaka dagacin Lamabata ne a ranar Asabar biyo bayan wata tarzoma.
Bello ya bada umarnin cewa

Dokar zata fara ne daga karfe 6:00am Zuwa 6:oopm farawa daga ranar Lahadi kuma har sai baba ta gani.
Ya kara da cewa an sanya dokar ne domin taimakawa jami’an tsaro su nemo bakin zaren matsalar, su tseratar da Rayukan Al’umma da dawo da doka da Odar.
Sanarwa ta kuma bayyana cewa Gwamnatin jihar tayi Allawadai da wannan tarzoma data auku a garin na lambata.
Ta kuma bukaci Al’ummar garin dasu bi doka domin baya jami’an tsaro damar dawo da zaman lafiya a garin.

PRNigeria hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1190 days 9 hours 16 minutes 15 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1172 days 10 hours 57 minutes 40 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com