Wani rahoto da aka fitar ya nuna cewa ‘yan Najeriya miliyan 25 na cikin barazanar faɗawa halin yunwa tsakanin watan Yuni da kuma Agustan 2023 muddin ba a dauki matakin gaggawa ba.
Rahoton wanda kungiyar Cadre Harmonisé ta fitar, wadda kungiya ce ta Majalisar Dinkin Duniya da ke taimakawa wajen samar da abinci mai gina jiki, ya nuna cewa ƙasar na ci gaba da fama da rikice-rikice da sauyin yanayi da kuma hauhawar farashin kayan abinci.
Read Also:
A cewar wata sanarwa ta haɗin gwiwa da hukumar noma da samar da abinci da asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya da hukumar bayar da agaji suka fitar, ta ce hakan ya nuna ƙaruwa a mutane miliyan 17 da ke fama da matsalar ƙarancin abinci a yanzu.
Sanarwar ta kuma lura cewa an ayyukan ‘yan ta-da-ƙayar-baya ya shafi aikin samar da abinci a yankin arewa maso gabas da suka hadar da jihohin Borno, Adamawa da kuma Yobe da kuma matsalar ayyukan ‘yan bindiga da garkuwa da mutane a Katsina da Sokoto da Kaduna da Benue da kuma Neja.
Sanarwar ta ce Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA, ta ruwaito cewa matsalar ambaliyar ruwa da aka samu a shekarar 2022, ya lalata kadada 676,000 na gonaki wanda kuma ya kawo raguwa a abin da mutane suka girba da janyo ƙaruwar barazanar matsalar ƙarancin abinci ga iyalai a faɗin kasar
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 14 hours 29 minutes 28 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 10 minutes 53 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com