An sami Faduwar Naira a kasuwar bayan Fage a Nijeriya

An samu faduwar darajar naira da kaso 1 da digo 1 cikin dari a kasuwar bayan fage.
Yanzu haka an samu hauhawar farashin dalar amurka, inda ake siyar da kowace dala daya a kan naira dari 7 da 48, a kasuwannin hada-hadar canjin kudaden ketare na bayan fage dake Najeriya.
Wani kwarya-kwaryan bincike da wata kafar yada labarai mai zaman kanta a Najeriya ta gudanar ya rawaito yadda ‘yan kasuwar bayan fage ke siyan kowace dala daya a kan naira 740 abin da ya alamta Karin kudin da aka saba siya a baya da naira 8.
Koda yake kawo yanzu binciken ya tabbatar da yadda ake siyar da kowace dala daya a farashin gwamnati a kan naira 461 a wani bincike da aka gudanar a ranar Talatar da ta gabata.

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com