Hukumar da ke Hana Sha da Fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA ta ce ta samu nasarar kama hodar ibilis da tabar wiwi da aka shiga ƙasar da ita daga ƙasashen Brazil da Canada a biranen Enugu da Legas.
Wannan na kunshe ta cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Femi Babafemi ya sanya wa hannu, inda tace ce hukumar ta kama ƙwayoyin tramadol miliyan 1.7 a birnin Legas da ke kudu maso yammacin ƙasar, tare da kama mutanen da ta daɗe tana nema a jihohin Osun da Kano da Ondo da Edo da Abuja babban birnin ƙasar.
Read Also:
Sanarwar ta ci gaba da cewa ”Jami’an hukumar NDLEA da ke aiki a filin jirgin saman Akanu Ibiam da ke Enugu da masu aiki a tashar jirgin ruwa na Tican da ke Legas sun samu nasarar daƙile yunƙurin shigo da kilogiram 126.95 na hodar ibilis da tabar wiwi ƙunshe cikin ƙwalayen ganyen shayi da ababen hawa daga Brazil da Canada”.
Sanarwar ta ƙara da cewa a filin jirgin saman Enugu an kama wani fasinja mai suna Eze Christian Ikenna mai shekara 42, da ya shiga ƙasar daga Brazil ranar 20 ga watan Janairun, bayan da aka binciki jakar da ya zo da ita inda ka samu hodar ibilis da ta kai nauyin kiligiram 16.2.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 17 hours 44 minutes 21 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 19 hours 25 minutes 46 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com