Hukumar tattara bayanan sirri kan harkokin kuɗi ta Najeriya ”Nigerian Financial Intelligence Unit” (NFIU) ta ce haramcin da take ƙoƙarin sanyawa kan cire kuɗi daga asusun gwamnatin tarayya da na jihohi abu ne da zai taimaka wa gwamnonin ba cutar da su ba.
Hukumar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar ta hannun jami’inta na hulda da jama’a Ahmed Dikko sa’o’i bayan ƙungiyar gwamnonin ƙasar ta soki sanarwa da hukumar ta fitar ranar 5 ga watan Janairu, ta umartar bankuna da su dakatar da bai wa gwamnoni kudaɗe daga asusun gwamnati daga ranar 1 ga watan Maris mai zuwa.
“Sabuwar dokar da hukumar NFIU ke shirin ƙaƙabawa game da sha’anin shige da ficen kuɗi baya cikin tsarin dokokin da ayyukan hukumar” Kamar yadda ƙungiyar gwamnonin ta bayyana a wata sanarwa da ta fitar.
Read Also:
Ƙungiyar gwamnonin ta kuma kafa kwamiti mai mambobi shida da za su tattauna da babban bankin ƙasar domin duba batun matsalolin sha’anin harkokin kuɗi da ƙasar ke fuskanta.
A martanin da hukumar ta NFIU ta fitar ta ce a shirye take domin hada kai da kwamitin da ƙungiyar gwamnonin ta kafa domin wayar musu da kai game muhimmancin sabon kuɗurin.
”Sannan abun da muke ƙoƙarin aiwatarwa bai saɓa doka ba. Mun bayar da ƙa’idar ne domin magance tarin bincike da muka hango wa gwamnonin. Mun sanya ƙa’idar ce domin taimaka wa gwamnonin ba don cutar da su ko wani ma’aikacin gwamnati ba” kamar yadda sanarwar da NFIU ta fitar.
Sannan kuma hukumar ta ce a baya ta sanya makamanciyar wannan doka kan ƙananan hukumomi, inda aka kai ta kotu, amma kuma sai ta yi nasara a kotun.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 19 hours 36 minutes 49 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 21 hours 18 minutes 14 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com