Dakarun sojojin Nijeriya sun sami nasarar hallaka mayakan ISWAP a yunkurin su na yiwa Sojojin kwantan bauna
Dakarun sojojin Nijeriya karkashin rundunar hadin Gwiwa ta 25 sun halaka mayakan ISWAP a mashigar Damboa dake jihar Borno a Arewa maso Gabashin Kasar.
Read Also:
Zagazola ya ruwaito cewa mayakan sun gamu da gamun su ne, bayan sun shirya yiwa dakarun sojojin kwantan Bauna a kauyen komala dake hanyar Damboa zuwa Maiduguri.
Sojojin sun sami nasarar kwato Motar da aka girke bindiga a kanta, MRAP, Babura da wasu muggan makamai.
PRNigeria Hausa