Shugaban Hukumar Zaben Najeriya Farfesa Mahmood Yakub ya ce za a gudanar da zabukan kasar da ke tafe kamar yadda aka tsara a wannan shekara ta 2023.
Yayin da yake jawabi a taron majalisar zartarwar kasar da Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta yau Laraba a fadar mulki da ke Abuja, Mahmood ya ce zaben shugaban kasa da ‘yan majalisar tarayya yana nan yadda aka tsara ranar 25 ga watan nan na Fabrairu.
Haka kuma shi ma zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar jihohi da za a yi ranar 11 ga watan Maris yana nan ba ja da baya kamar yadda aka tsara yi, in ji shugaban na INEC.
Shugaban hukumar zaben ya bayyana gaban majalisar ne yayin da ya rage kwana 17 a fara zabukan, domin ya yi bayani kan halin da ake ciki game da shirye-shiryen hukumarsa.
Read Also:
Da yake zantawa da manema labarai bayan fitowa daga zauren majalisar, Farfesa Yakubu ya ce ya bayyana ne gaban majalisar ministocin domin sanar da ita irin shirin da hukumar ta yi na gudanar da manyan zabukan na bana.
Ya kara da cewa daman abin da aka saba yi ne a duk lokacin da ake daf da zabe a kasar, shugaban hukumar ya yi wa majalisar zartawa bayani inda shirye-shiryen suka kwana.
Sai dai akwai wasu matsaloli guda uku da a baya hukumar ta ce ka iya yin tarnaki ga gudanar zabukan, matsalolin da suka kunshi rashin tsaro da karancin takardun kudi da kuma man fetur.
Ko baya ga yin wannan bahasin gaban majalisar ministocin, ana sa ran shugaban hukumar zaben ya sake bayyana gaban majalisar magabata ta kasa wato Council of State ranar Juma’a, domin sanar da ita a hukumance irin yadda hukumarsa ta kintsa domin gudanar da manyan zabukan.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 12 hours 45 minutes 58 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 14 hours 27 minutes 23 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com