Kungiyar Makarfi Ambassadors ta bayyana hukuncin da kotun koli ta ‘yanke kan shari’a Machina da Ahmad Lawan matsayin rashin adalci
Read Also:
Kungiyar wacce kungiya ce dake goyon bayan babbar jam’iyyar hamayya ta Nijeriya PDP, wanda tace ta lura cewa alkalai uku na kotun da suka yi watsi da hukunce-hukuncen farko na babbar kotun tarayya da kotun daukaka kara ba su taimaka wa dimokradiyyar kasar ba.
Kungiyar tace, wannan hukunci ba abin razanarwa bane kai dai, lamari ne marasa dadi ga damukradiyya.
A ranar litinin din data gabata ne kotun kolin kasar ta yanke hukunci kan shari’ar dake tsakanin shugaban majalisar dattawa da Bashir Machina, bisa sahihancin wanda ya kamata ya yiwa jam’iyyar sa ta APC takarar wakilcin yankin Yobe ta Arewa, hukunci da ake kallon an yiwa Ahmad lawan Alfarma a cikin sa.
Tunda fari dai kuton Tarayya a Damaturu da kotun daukaka kara da ke Abuja sun yanke hukuncin daya bawa Machina nasara.
Da take mayara da martani ta cikin wata takardar sanarwa mai dauke da sa hannun kodinetan kungiyar kan al’amurra na musamman Mr. Abdullahi Ahmad da kodinetan shiri da tsare-tsare Engr. Bolade Aina, kungiyar ta bayyana takaicinta, inda tace Sanata Ahmad lawan bai shiga zaben fidda gwani na jam’iyyar APC da aka kudanar a jihar Yobe ba, zaben daya tabbatar da machina matsayin wanda yayi nasara.
Makarfi Ambassadors sunce “a fahimtarsu da dokokin zabe, wajibi ne dan takara ya shiga zaben fidda gwani da jam’iyyun su suka hada.
“Amma yaya tunani zai yadda da ganin an bawa wanda bai taka rawa a gas aba lambar yabo kwatankwacin wadanda suka fafata a gasa?’
“kananan kotunan da suka yanke hukunci a kan wannan Al’amari, a ganinmu, sun yi abin da ya kamata. Haka kuma Alkalan kotun Koli su 3 da suka yi watsi da hukunce-hukuncen ta bayyana karara basu taimaki damukradiyya ba.
Abinda muka dauka matsayin mataki kuma shi ne, bangaren shari’a, musamman ma koli a karkashin jam’iyyar APC mai Mulki ba zai zama mafita ta karshe ga talakawan kasar ba.
Idan dai za’a iya tunawa wani hukuncin kotin kolin makamancin wannan daya bawa Hope Uzodinma nasara wanda kuma shine na 4 a zaben da aka fafata a jihar ta Imo.
Don haka muna kira ga ‘yan Nijeriya dasu fatattaki jam’iyyar APC, ta hanyar zaben jam’iyyar Adawa ta PDP domin cancantar ta.
PDP it ace kadai jam’iyya dake mutunta doka, ta kuma nuna an gani a kasar lokacin data rike shugabancin kasar tsahon shekaru 16.
A jihar kaduna Makarfi ambassadors ta bukaci Al’ummar jihar dasu zabi Hon Isa Ashiru kudan domin ceto jihar daga halin da take ciki.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 14 hours 49 minutes 33 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 16 hours 30 minutes 58 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com