Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta soki gwamnatin tarayya kan ƙarancin Kuɗi da na man fetur da ake fama da shi a faɗin ƙasar.
Wannan na kunshe ta ciki wata sanarwa da shugaban ƙungiyar Emmanuel Osodeke ya fitar ya ce gwamnatin ƙasar a matakan tarayya da jihohi da kuma ƙananan hukumomi na aiwatar da tsare-tsaren da suke wahalar da talakawan ƙasar.
Ya ƙara da cewa matakin da Kotun Ƙolin ƙasar ta ɗauka na dakatar da aiwatar da wa’adin 10 ga watan Fabrairu na daina amfani da tsofaffin takardun kuɗi, zai taimaka wajen sauƙaka wa ‘yan ƙasar halin matsin da suke ciki.
Read Also:
Mista Osodeke ya ƙara da cewa tsarin da gwamnan CBN Godwin Emefiele ya ɓullo da shi na ”hana walwalar kuɗi” an taɓa yin sa a Indiya a shekarar 2016 wanda ya haifar da wahalhalu a ƙasar.
“Dan haka, ASUU tana yaba wa Kotun Ƙoli da wannan hukunci ta hanyar la’akari da halin da talaka ke ciki wanda Emefiele ya jefa su ciki”, in ji Osodeke.
A makon da ya gabata ne dai Kotun Kolin ƙasar ta dakatar da Babban Bankin ƙasar aiwatar da wa’adin 10 ga watan Fabrairu na daina amfani da tsoffin kuɗin, bayan da wasu jihohin ƙasar uku suka shigar da ƙara gaban kotun.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1240 days 13 hours 30 minutes 21 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1222 days 15 hours 11 minutes 46 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com