Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayar da umarnin rufe kwalejojin fasaha a faɗin ƙasar gabanin babban zaɓen ƙasar da ke tafe ranar 25 ga watan Fabrairu da 11 ga watan Maris da ke tafe.
Ministan Ilimin ƙasar Adamu Adamu ne ya sanar da haka cikin wata wasiƙa da jami’in ma’aikatar I.O Folorunsho ya sanya wa hannu, tare da aike wa babban sakataren hukumar kula da kwalejojin fasaha na ƙasa (NBTE) Idris Bugaje.
Ministan ya umarci shugabannin makarantun duka kwalejojin fasaha cewa a tsadar da karatu daga 22 ga watan Fabrairu zuwa 14 ga watan Maris.
Read Also:
Wasiƙar ta ci gaba da cewa ”Sakamakon fargabar da ake da ita kan tsaron tsaron malamai da ɗalibai da kadarorin makarantunmu, Ministan Ilimi Adamu Adamu bayan tuntuɓa mai zurfi da hukumomin tsaro, ya bayar da umarnin rufe duka makarantun fasahar”
”Dan haka za a rufe makarntun daga ranar Laraba 22 ga watan Fabrairu zuwa 14 ga watan Maris 2023,”
A makon da ya gabata ne dai Hukumar Kula da Jami’o’i ta Najeriya ta bayar umarnin a rufe dukkanin jami’o’in ƙasar tsawon lokacin da za a gudanar da babban zaɓen ƙasar na 2023.
A wata sanarwar mai ɗauke da sa hannun mataimakin shugaban hukumar, mai kula da harkar gudanarwa, Chris J. Maiyaki, ya ce za a rufe jami’o’in ne domin kare lafiyar ma’aikata, da ɗalibai a tsawon lokacin zaɓen.
Bayanin ya ce umurnin ya fito ne daga ministan ilimi na Najeriyar, Adamu Adamu, inda aka umurci dukkanin shugabannin jami’o’i su rufe daga 22 ga watan Fabrairu zuwa 14 ga watan Maris.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 23 hours 1 minute 55 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1237 days 43 minutes 20 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com