zaben 2023- NRC ta dakatar zirga-zirgar Jiragen kasa a Nijeriya

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen ƙasa ta Najeriya za ta dakatar da sufurin jiragen ƙasa a faɗin ƙasar na wucin-gadi gabanin babban zaɓen ƙasar da ke tafe.

Wannan na kunshe ta cikin watar  sanarwar da hukumar ta fitar mai ɗauke da sa-hannun mataimakin daraktan yaɗa labarai na hukumar Yakub Mahmood.

sanarwa tace hanyoyin jiragen ƙasan da dakatarwar za ta shafa sun haɗa da Abuja zuwa Kaduna da Warri–Itakpe da Lagos–Ibadan, da kuma hanyar Iddo Lagas-Ijoko.

Haka ta ce ta ɗauki matakin ne domin bayar da dama ga ‘yan ƙasar su gudanar da zaɓukan dake tafe ‘yan kwanaki masu zuwa.

Sanarwar ta kara da cewa Dakatarwar wucin-gadin za ta fara ne daga ranar 25 zuwa 27 ga watan Fabrairun da muke ciki, kamar yadda yake kunshe cikin sanarwar da hukumar ta fitar.

“Haka kuma, hukumar na sanar da al’umma cewa za a maido da zirga-zirgar jiragen ƙasan daga ranar Talata 28 ga watan Fabrairu.

PRNigeria hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1245 days 15 hours 58 minutes 15 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1227 days 17 hours 39 minutes 40 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com