Jami’an ‘yan sandan Finland sun cafke Simon Ekpa, wani mai rajin kafa kasar Biafra wanda kuma ya sha yin barazanar hana gudanar da zaben 2023 a Najeriya.
Ekpa ya jima yana furta kalaman tunzuri domin haddasa tashin hankali a Najeriya daga can mazauninsa a na kasar Finland.
Read Also:
Ekpa ya sha yin kira ga mutanen yankin kudu maso gabashin Najeriya da su rika mutunta umarnin Kungiyar IPOB na zaman gida kan tilas a kowanne mako, abin da ya kara fito da manufarsa ta neman raba kan Najeriya.
Kafin cafke shi a wannan Alhamis, gwamnatin Najeriya ta rattaba hannu kan wata takardar korafi domin ganin an cafke mutumin da ke goyon bayan ballewar kabilar Igbo daga kasar.
PRNigeria hausa