Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe iyakokin ƙasar na sa’a 24 gabanin babban zaɓen ƙasar da ke tafe a ranar Asabar.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Hukumar Shige da Fice ta Najeriya ta wallafa a shafinta na tiwita wanda ya samu sa hannun shugabanta, Isah Jere Idris.
Read Also:
Sanarwar ta ce daga ranar Asabar za a rufe dukkan iyakokin ƙasar na ƙasa har zuwa ranar Lahadi 26 ga watan Febrairun 2023.
Idris Jere ya buƙaci dukkan shugabannin hukumar da ke kan iyakoki da su tabbatar an bi sahun wannan umarni.
Ya ce hukumar a shirye take wajen ganin ta bayar da gudummawa na ganin an gudanar da zaɓukan ƙasar lami lafiya.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1245 days 15 hours 49 minutes 14 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1227 days 17 hours 30 minutes 39 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021
Report By: PRNigeria.com